Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Wannan taron ya samu halartar malamai daga ƙasashe 9 (Panama, Colombia, Trinidad da Tobago, Iraq, Lebanon, Syria, Algeria, Palestine, India da Yemen) Wanda aka gudanar da shi a birnin Qom, Cibiyar Kimiyya da Al'adu ta Al-Khalq Al-Azim. Muhimman abubuwan da aka gabatar a taron:
Manufofin haɗin gwiwa: Daraktan Cibiyar Al-Khalq Al-Azim ya jaddada muhimmancin "ɗabi'a bisa ga hankali" a cikin ayyukansu kuma ya bayyana fatan cewa wannan taron zai zama farkon haɗin gwiwa da Ustan Quds Razawi.
Manyan Bayanai Da Aka Gabatar:
1. Darajar Dan Adam shine babban Babban Jigo a taron:
Wanda akai binciken darajar mutum da aka samo daga ayar "Kuma hakika mun girmama 'ya'yan Adam" wanda (Dr. Linda Tabush, Lebanon) ya gabatar.
Ya tabbatar da darajar zama ɗan ƙasa, 'yancin ilimi, da komawa ƙasarsa a rayuwar Razavi.
2. Adalci na zamantakewa da tattalin arziki:
Yaƙi da Talauci wanda ya zama a matsayin Aikin Addini wanda talauci ya zama Rashin Lafiyar Ruhaniya wanda (Tamam Al-Washli, Yemen) ta gabatar.
Adalci na Tattalin Arziki da Haƙƙin Kadarori ya Mayar da Hankali Kan Haramcin Zalunci da Tallafawa Adalci (Ishaq Al-Washli, Yemen)..
Tallafawa gungun alummar da akai watsi da su (Marasa Lafiya, 'Yan tsiraru, Baƙi, 'Yan Gudun Hijira). A mahangar Imam Ridha as wanda (Ali Abdul Hakim, Colombia) ya gabatar.
3. Siyasa da Mulki:
Shugabanci Mai daukar nauyi da Alhaki da yin Hidimar Jama'a Bisa Ka'idodin Ɗabi'a a mahangar Imam Ridha as wanda (Sayyid Taha Mujahid, Yemen) ya gabatar.
'Yancin Siyasa a Zamanin Imam Ridha as. da kuma musharakar daidaikun mutane daga cikin al'umma wanda (Mujtaba Al-Halily, Yemen) ya gabatar.
Tsarin fuskantar zalunci da la'antar azzalumi da kuma bayyana nauyin tsayawa tsayin daka a kansa wanda (Abbas Shahid Abdul-Latif, Trinidad da Tobago) ya gabatar.
4. Tattaunawa Da Hankali:
Matsayin hankali da kuma amfani da shi a cikin muhawarorin da Imam Riza (AS) ya gabatar tare da mabiya addinai da ƙungiyoyi daban-daban wanda (Yasmina Zabih, Aljeriya) ta gabatar.
Haɓaka tattaunawa tsakanin al'adu bisa daidaito da girmamawa (Zikri Al-Rashidi, Yemen)..
5. Batutuwan Jin Kai Na Zamani:
Alakar koyarwar Imam Riza da wahalar yara da mata a Gaza da kuma jaddada adalci na zamantakewa da kare marasa galihu wanda Malama (Rima Sheikh Qassem, Falasɗinu) ta gabatar.
6. Iyali Da Muhalli:
Haƙƙoƙin iyali a matsayin cikakken samfuri abun koyi na mutuncin ɗan adam da tsaron zamantakewa Malama (Fatima Azadimanesh, Siriya da Waad Al-Awta, Lebanon).
Yanayin zamantakewa na muhalli da alhakin ɗan adam a cikin koyarwar Imam Riza wanda (Amin Rabih, Yemen) ya gabatar.
Dukkan bayanai da Takardun da aka gabatar a wajen taron sun jaddada ma'anar cewa koyarwar Imam Ridha (AS). Tana ba da cikakken tsari kuma na zamani ba kawai ga Musulmai ba, har ma ga dukkan bil'adama a fannoni na haƙƙin ɗan adam, mutuncin ɗan adam, adalci na zamantakewa, shugabanci na ɗabi'a, da kuma zaman lafiya tare, kuma yana iya zama mafita ga ƙalubalen da yawa na duniyar yau.
Your Comment